Shugaban kungiyar ta Hizbullah yana magana ne dangane da zagayowar ranar Qudus ta duniya wacce zata kasance gobre 7 ga watan Mayu, wato jumma’a na kasar na watan Ramalana kamar yadda Imam Khomaini (q) wanda ya kafa jumhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana.
Sayyeed ya kara da cewa alamun faduwar da kuma wargajewar haramtacciyar kasar Isra’la sun bayyana tare da faduwar ‘Yarjejeniyar karni’ da kuma gwamnatin Donal Trump na kasar Amurka.
Ya ce a halin yanzu kasashe da kungiyoyi masu gwagwarmaya ne zasu ayyana makomar yankun kudancin Asia. Sannan sajewar da wasu shuwagabannin kasashen larabawa suka yi da haramtaccikar kasar ba abinda ya kara mana sai kara tabbata a kan goyon bayan al-ummar Falasdinu a gwagwarmayan da suke yi da yahdawan sahyoniyya ‘yan ammaya.
Har’ila wannan wannan ya dada nauyin da ke kammu na ganin cewa an ‘yentar da masallacin Qudus. Dana karashe shugaban ya bayyana cewa musulmi a ko iana suke, duk tare da matsalolin cutar Korona da ake fama da ita su nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu ta duk wata hanya da ta sawwaka a garesu.
342/